‘Yan sandan Jihar Delta, sun kama mutane shida tare da kwato wasu miyagun ƙwayoyi , ciki har da Tramadol da Rohypnol, bayan wani samame a wani waje da ake zargin ana sayar da  miyagun ƙwayoyi a Agbor, karamar hukumar Ika ta Kudu.

Kakakin rundunar, SP Bright Edafe, ya ce jami’an suna sintiri na yau da kullum a titin Alegwe, kusa da titin Owa, sahihan bayanan sirri suka iske inda suka yiwa wajen tsinke tare da kamo wadanda ake zargin.

SP Edafe ya ce bayan faɗaɗa bincike kan wani abin hawa ne jami’an suka gano wani sinƙin ƙwayoyin Tramadol, Rohypnol da wasu sinadarai da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne a cure waje guda.

Kakakin ‘Yan sanda ya ce suna tsare da waɗanda ake zargin da kuma kayan laifin, yayin da masu bincike ke ƙoƙarin gano inda ƙwayoyin suka fito.

Haka kuma suna binciken irin rawar da kowane ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya taka da kuma ko lamarin na da alaƙa da wata babbar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *