Ƙungiyar Kano Pillars ta lallasa Niger Tornadoes da ci 3-2 a wasan mako na biyu na Gasar Firimiyar Najeriya ta (NPFL) a wasan da suka buga a ranar Lahadi, a filin wasa na Sani Abacha dake KofarMata, Kano, a ranar Lahadi.
Pillars, wadda ake mata laƙabi da ‘Sai Masu Gida’, ta zura ƙwallaye biyu da nema ta hannun John Ubong Friday a minti na 40 da kuma ƙwallon da Fabian Nworie ya ci a minti na 45 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Dawowa daga hutun rabin lokaci ke da wuya, mai masaukin baƙi ta ƙara zura ƙwallo ɗaya a raga, inda Fabian Nworie ya zura ƙwallonsa ta biyu a karawar.
-
Za mu fuskanci wasan mu da Spaniya kamar wasan ƙarshe – Kocin matan Najeriya
-
Arsenal ta doke Chelsea 2-1 a babban wasan Landan
-
Shooting Stars ta lallasa CS Sfaxien a wasan farko na Gasar CAF Confederation Cup
Niger Tornadoes ta canza akalar wasan, yayin da ta farfaɗo daga baya inda ɗan wasa Joseph Godfrey ya nuna ƙwazonsa ya zura ƙwallo biyu shi kaɗai a mintuna na 72 da kuma 88.
Tornadoes ta yi ƙoƙarin farke duka ƙwallayen da aka zura mata, amma Pillars ta jajirce wajen tabbatar da samun narasa a fafatawar, inda a yanzu take mataki na uku da maki huɗu a teburin Gasar Firimiyar Najeriya.
A wani wasan na daban, ƙungiyar Plateau United ta garin Jos, ta doke Kwara United da ci 1-0 mai ban haushi a wasan da suka buga a sabon filin wasa na garin Jos, a ranar Lahadi.
Tun a minti na 29, ɗan wasa Alex Aghahowa Otakho, ya zura ƙwallon da ta bai wa mai masaukin baƙi nasara duk da hare-haren da Kwara United ta kai domin farke cin da aka yi mata.
A garin Lafiya, bayan shan kaye a wasan farko, Nasarawa United ta doke Bendel Insurance da ci 1-0 inda ta haɗa maki uku daga wasanni biyu da ta buga.
Ɗan wasa Pam Samuel, ne ya zura ƙwallon da ta tabbatar wa masu masauƙin bakin nasara a minti na 55.
Ga cikakken sakamakon wasannin da aka buga na ranar Lahadi, na mako na biyu na Gasar Firimiyar Najeriya:
Kano Pillars 3-2 Niger Tornadoes
Kun Khalifat 0-0 Barau FC
Nasarawa United 1-0 Bendel Insurance
Plateau United 1-0 Kwara United