Kotu tace Jonathan za iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta dage sauraron karar da ake kalubalantar cancantar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan na tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Wannan mataki ya biyo bayan rashin halartar zaman kotun da mai shigar da karar Emmanuel Agida, da kuma wakilan wanda ake kara na farko wato hukumar zabe ta kasa (INEC) suka yi a yau.

Kotu ta dage zaman sauraron karar  zuwa ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2026, da karfe biyu na rana (2:00pm) .

A ranar 28 ga watan Afrilun shekarar 2026 ne Mai Shari’a Peter Lifu ya bayar da umarnin isar da takardar sammaci ga wadda ake kara na biyu wato Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bayan da suka gaza mika bayanan kariyarsu a kan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *