Rundunar Sajin Najeriya ta dakile wasu jerin hare-hare a jihohin Borno, Zamfara da Filato, tare da hallaka ‘yan bindiga masu tarin yawa da kama wasun daga ciki.

A jihar Borno, dakarun runduna ta 27 ne suka dakile wani kwanton-bauna da ‘yan ta’adda suka yi musu a hanyar Buni Gari zuwa Buratai a karamar hukumar Biu a maraicen ranar Litinin.

Duk da cewa motar sojin kirar MRAP ta taka ma’adinai da ke binne inda tayoyin ta biyu suka lalace, Sojojin sun kwace alburusai da makaman harba roka, babur da kekuna, rahotanni sun ce babu sojan da ya rasa ransa.

Har ila yau, dakarun bataliya ta 19 sun lalata wasu ababen fashewa da aka binne a hanyar Damboa-Bulabulin-Maiduguri kusa da Asorok, tare da ceto fararen hula da dama.

Sa’annan a yankin Pulka, cikin karamar hukumar Gwoza, dakarun Operation HADIN KAI tare da tallafin rundunar sojin sama da na CJTF, sun fuskanci harin da kungiyar ISWAP ta kai kansu, inda sojojin suka hallaka ‘yan ta’addan ta hanyar amfani da jiragen sama masu sulke, koda yake soja guda ya samu rauni a hannunsa.

A jihar Zamfara kuwa, rundunar Operation FANSAN YANMA ce ta kaddamar da hare-hare ta sama a yankin Yankuzo da ke karamar hukumar Tsafe, inda jiragen soji biyar suka kai farmaki kan maboyar ‘yan bindiga.

Farmakin ya yi sanadiyyar hallaka ‘yan ta’adda da dama, ciki har da makusancin hatsabibin dan bindigar nan Musa Kwamanda da ake yiwa lakabi da Isiya Gurgu, babu asarar rai a bangaren sojin ko farar hula.

Haka kuma a jihar Filato, dakarun Operation Enduring Peace (OPEP) sun gudanar da wani sumame a Shinko road kusa da sabon Gidan Gwamnati a Jos ta kudu, an cafke ‘yan ta’adda 14 da tarin makamai.

Dukkanin wadannan hare-hare, sun faru ne daga maraicen Litinin 7, zuwa wayewar garin Talata 8 ga watan Satumbar 2026, kamar yadda Shafin masani kan tsaro Zagazola Makama ya ruwaito.

Rundunar sojin ta yi fatan al’umma zasu cigaba da bata haɗin kai domin tabbatar da muradin ta na wanzuwar zaman lafiya da walwala a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *