Tsohon ɗan wasan Ivory Coast, Yaya Touré, ya kafa sabon tarihi bayan ya zama ɗan Afirka na farko da ya jagoranci wata ƙungiya zuwa matakin gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League a matsayin babban koci.
Touré ya cimma hakan ne tare da zakarun Slovakia, Slovan Bratislava, bayan da ƙungiyar ta doke NK Celje ta Slovenia da ci 2-1 bayan karin lokaci, inda ta samu nasarar tsallakewa da ci 3-2 jumulla.
- NFF ta naɗa Eguavoen kocin wucin gadi na Super Falcons
- Najeriya za ta kara da Russia a wasan sada zumunta
Touré, mai shekaru 43, wanda aka nada kocin Slovan Bratislava a watan Yuni, ya jagoranci ƙungiyar ta tsallake zagaye uku na neman gurbin shiga gasar, duk da cewa wannan shi ne karon farko da yake jagorantar ƙungiya a matsayin babban koci.
Nasarar ta zarce abin da ɗan Najeriya Ndubuisi Egbo ya samu a shekarar 2020, lokacin da ya jagoranci KF Tirana ta Albania a wasannin neman gurbin Champions League, amma ƙungiyar ba ta kai matakin gasar ta ƙarshe ba.
Yanzu Touré zai sake komawa gasar Champions League, amma wannan karon a matsayin koci, inda Slovan Bratislava za ta fuskanci Paris Saint-Germain.
Touré ya lashe kofin Champions League a 2009 a matsayin ɗan wasa tare da Barcelona, kuma yanzu zai nemi kafa wani sabon tarihi daga kujerar koci.