Shugaban Jam’iyyar APC Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fara hutun makonni biyu a kasar waje, domin hutawa gabanin tunkarar kamfe na babban zaben 2027.

Cikin wata sanarwa da Babban Mashawarcin sa kan yada labarai Abimbola Tooki, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, yace hutun zai baiwa Yilwatda damar wartsakewa da kuma sake tunkarar nauyin da ke kansa gabanin zabuka masu zuwa.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban na APC ya shafe shekarar da ta gabata yana gudanar da ayyukan jam’iyya mau tarin yawa, da suka hada da tsare-tsare, tafiye-tafiye, da tarurrukan yada angizo da dabarun siyasa, da nufin sake fasalin jam’iyya mai mulki.
Tun bayan karbar ragamar mulkinsa, Yilwatda ya yi aiki kafada da kafada da Kwamitin dattawa, gwamnoni, mambobin Majalisar Tarayya, Shugabannin jam’iyya na jihohi, zababbun da dukkanin masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta maida hankali kan nasarorin da aka samu, ciki har da nasarar shiryawa da kammala babban taron APC na Kasa, sake fasalta tsarin gudanarwa, da kuma gudanar da zaben fitar da gwani a matakai daban-daban.
Jam’iyyar ta jaddada cewa kada a fassara hutun Yilwatda a matsayin ajiye aiki ko sakaci da nauyin da ke kansa, inda ta bayyana shi a matsayin “dama ce ta janye jiki kadan daga ayyukan yau da kullum, domin daukar sabon karfi da tunani a kan nauyin da ke gaba.”
A cewar sanarwar, shugaban na APC zai kuma yi amfani da wannan lokaci wajen fito da sabbin dabaru, bullo da sabbin hanyoyin ciyar da jam iyyar gaba, da tsare-tsaren taron kwamitin dattawan jam iyya mai zuwa, wanda zai tabo sabbin kalubale, da kuma cimma matsaya kan dabarun da za a bi a watanni masu zuwa.
APC ta bayyana cewa rashin kasancewar shugaban Yilwatda a kasar ba zai shafi tafiyar da harkokin jam’iyyar ba, kasancewar kwamitin dattawan ta zai ta ci gaba da aiwatar da nauyin da ke kanta bisa tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da hanyoyin da aka saba bi.
Ana sa ran Yilwatda, zai dawo Najeriya a karshen hutun na makonni biyu domin ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum.