Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta ƙaddamar da wani sabon yunƙuri na ƙasa baki ɗaya domin kawo ƙarshen lodin fiye da kima, da kuma inganta amfani da hanyoyin mota a Najeriya.
An ƙaddamar da yunƙurin ne a Abuja, yayin wani taron wayar da kai mai taken “Ending Overloading, Saving Lives: A National Commitment to Safer Roads and Responsible Transportation in Nigeria.”
Taron ya haɗa hukumomin gwamnati da masu harkar sufuri da masu kaya, hukumomin sa ido, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai.
Shugaban Hukumar kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, Shehu Mohammed, ya ce lodin kaya fiye da kima ba laifin da ya sabawa dokokin hanya kadai ba ne, laifi ne wasa da rayuwar al’umma dake amfani da hanyoyi, wanda ke haifar da lalacewar ababen hawa da ci gaban tattalin arziki.
- NDLEA ta cafke wani da ake zargi da safarar hodar Iblis mai nauyin kilogiram 49.70
- Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama mutum biyu bisa zargin kisa
- ‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yaɗa jita-jitar rufe kamfanin OPay
Ya ce, lodin wuce kima na rage ingancin abin hawa, sannan ya yi gargadin cewa haɗa fasinjoji da kaya waje daya kan haifar da mummunar barazana, a duk lokacin da wata matsala ta faru.
A cewarsa, babu wata riba ko rage kuɗin sufuri da ya kai darajar rayuwar ɗan Adam, a saboda haka dole ne masu abin hawa da fasinjoji, hukumomin dake sa ido da gwamnati su ɗauki nauyin tabbatar da tsaron rayukan matafiya.
FRSC, ta ce za ta ƙara ƙarfafa bincike da hukunta masu karya ƙa’ida da wayar da kan jama’a da amfani da bayanan sirri, tare da mayar da hankali kan agajin gaggawa bayan afkuwar haɗari zuwa matakan rigakafi.
Hukumar ta kuma ce bai kamata taron, ya tsaya kan rattaba hannu ba, sai dai ya zama yarjejeniyar aiki tare da kuma nauyi da wa’adin aiwatarwa da tsarin bibiyar sakamako.