An yi kiran cewa Gwamnatin Tarayya da bankunan da ke tallafa wa ci gaban masana’antu su binciki hanyoyin sake tsara basussukan da ke kan masana’antun auduga da saka da ɗinki da ke fuskantar matsaloli kafin su kai ga rufe su gaba ɗaya.

Wannan yana da mahimmanci wajen kare ayyukan yi da sake gina turbar masana’antun Ƙasar Nijeriya.

Mamba a Taron Haɓaka Ɓangaren Auduga dabSaka, da Ɗinki (CTGDF), Dr. Bello Salman, shi ne ya yi wannan kiran a Abuja, inda ya jaddada cewa ƙoƙarin maida basussuka bai kamata ya kasance ta hanyar lalata masana’antun da za su iya ci gaba da aiki da kuma al’ummomin da suka dogara da su ba.

Dr Bello Salman ya bayyana cewa rushewar masana’anta guda ɗaya yana shafar dukkan hanyoyin sarrafawa—tun daga manoman auduga da masu harkar sufuri, ma’aikatan masana’anta da masu samar da kayayyaki, har zuwa masu saƙar tufafi.

Ya ƙara da cewa ko da yake Bankin Masana’antu (BOI) da sauran cibiyoyin kudi na gwamnati suna da alhakin dawo da kuɗaɗen jama’a, ya kamata masu biyan bashi su fara tabbatar da ko masana’antar da ke fuskantar matsi za ta iya komawa kan turbar samun riba.

A cewarsa, sayar da na’urorin kera kaya na musamman da filayen masana’antu cikin gaggawa na iya samar da saurin dawo da bashi na ƙanƙanin lokaci, amma yana iya lalata kadarorin da ake buƙata don farfado da masana’antun ƙasar baki ɗaya.

Matsayinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin sake farfado da ɓangaren auduga, da saka, da ɗinki.

Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta amince da kafa Hukumar Haɓaka Auduga da Saka da Ɗinki a ƙarƙashin Shugabancin Ƙasa kuma mai zaman kanta a watan Afirilun 2025, inda ake sa ran samun kuɗaɗen gudanarwa daga harajin kayayyakin saka da ake shigowa da su daga waje.

Dr Bello Salman ya ce ya kamata shirin ya maida hankali wajen sake gina tsarin sarrafawa na sarrafa auduga da ke haɗe, inda manoma ke samar da datsa ga gidan kaɗa auduga, gidan kaɗa auduga yana samarwa masana’antar saka, sannan masana’antun sarrafa kaya suna samarwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

Ya ba da shawarar ƙirƙirar tsarin farfadowa da sake tsara masana’antu inda masana’antun da ke fuskantar kalubale za su fuskanci bincike mai zaman kansa na fasaha da kuɗi da doka, da kasuwa kafin a yanke shawarar rushe su.

Ya ce wadannan binciken ya kamata su tabbatar da yanayin injuna da, samun ɗanyen kayan aiki da buƙatun ƙarfin wutar lantarki da damar kasuwa da nauyin bashi, da yuwuwar jawo sabbin masu zuba jari.

Ga masana’antun da aka samu da yuwuwar ci gaba, Dr Bello ya ba da shawarar sake tsara bashi da  gyara injuna da inganta tsarin gudanarwa da samar da sabbin kuɗaɗen gudanarwa da haɗin gwiwa tsakanin masu zuba jari na dabarun gaske da gogaggun ma’aikata.

Sai dai kuma, ya ce kamfanonin da suka gaza cika ma’aunin yuwuwar ci gaba kada su ci gaba da samun tallafin gwamnati na har abada, inda ya ƙara da cewa dole ne a haɗa sake tsarin da sakamako mai ƙididdiguwa.

Ya kuma yi kiran da a ƙara ƙarfafa tallafi ga manoman auduga ta hanyar samar da ingantattun irurruka da kayayyakin aiki a kan lokaci da ayyukan fadakarwa da na’urorin zamani da kuma kasuwanni masu tabbaci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *