Wasu jerin hare hare a bututun man Saudi Arabiya wato East-West Pipeline dake Riyadh da Madina sun tilastawa hukumomin ƙasar dakatar da aiki na ɗan wani lokaci.
Ma’aikatar Makamashi ta ƙasar ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a, inda ta ce hare-haren da aka kai a safiyar Alhamis sun jikkata wasu mutane, waɗanda aka kai su asibiti domin samun kulawar lafiya.
Ma’aikatar ta ce nan take aka tura jami’an agajin gaggawa da ƙwararrun fasaha domin tabbatar da tsaron bututun da kuma tantance lafiyarsa, tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa.
- Iran na son kawar da ni-Trump
- Hutu da Tutsi: Rwanda ta tuna da waɗanda suka rasu a kisan kiyashin 1994
- An kama ‘yan Burundi 134 a Tanzania bayan tsaurara matakan shige da fice
Ta ƙara da cewa an rufe bututun ne a matsayin matakin kariya, inda ta ce za a sanar da duk wani sabon ci gaba idan ya samu.
A farkon wannan makon kuma, ƙungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran ta kai hare-hare kan ababen more rayuwa na fararen hula da kuma cibiyoyin makamashi a biranen Abha da Khamis Mushait da Jazan da Najran na Saudiyya.
Ma’aikatar Makamashin Saudiyya ta ce hare-haren sun haddasa gobara a wasu cibiyoyin mai da ke kudancin ƙasar, lamarin da ya tilasta dakatar da wasu ayyuka na wani ɗan lokaci.
A nasa bangaren, Kungiyar Haɗin Gwiwa ta Tallafawa Halaccin Gwamnati a Yemen ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai Saudiyya, waɗanda suka jikkata fararen hula 73, ciki har da mata da yara.
Ƙungiyar ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace domin kawar da barazanar.