Ahalin yanzu, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mai yiwuwa Iran ce ke da alhakin harin da aka kai kan bututun mai na East-West da ke Saudiyya.
Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da takwararsa ta Ireland, Catherine Connolly, a birnin Dublin, yayin wata ziyarar karshen mako da ya kai kasar, wadda ta hada da halartar wata babban gasar wasan golf da ake gudanarwa a filin wasan da yake da shi a gabar tekun Atlantika.
- Saudiyya ta rufe bututun mai na East-West bayan hare-hare
- Aljeriya ta rufe sararin samaniyarta ga Abdu-Dhabi
- Iran na son kawar da ni-Trump
Trump ya ce: “Komai zai warware cikin sauki,” yayin da yake magana a Dublin bayan ganawarsa da Connolly.
Trump ya bayyana cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, “aboki ne na kud da kud”, yana mai cewa komai zai “warware cikin sauki” lokacin da aka tambaye shi ko zai iya taimakawa wajen tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin ruwan Hormuz, sakamakon sabbin damuwar da suka taso dangane da Saudiyya.
Trump ya kuma ce yakin da ake yi da Iran zai kawo karshe ne bayan zabukan tsakiyar wa’adin Majalisar Dokokin Amurka.