Hukumar Fito ta Najeriya (NCS) da Hukumar Gudanar da Fito ta Jamhuriyar Benin sun ciyar da tsare-tsaren sauƙaƙe harkokin kasuwanci tsakanin su gaba ta hanyar gudanar da binciken haɗin gwiwa a kan iyakokin su na Seme da Krake domin zamanantar da binciken kan iyakokin su.
An gudanar da binciken ne a ranar Juma’a, 11 ga Satumba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Babban Shugaban Hukumar Fito ta Najeriya (CGC), Adewale Adeniyi, da Darakta Janar na Hukumar Fito ta Jamhuriyar Benin, Kwanal Raouf Aboudou.
Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar, CGC Adeniyi ya bayyana cewa wannan shirin yana nuna sabon matsayi na yarda da amincewa tsakanin ƙasashen biyu, sannan yana sanya Hukumar Fito a gaba wajen ciyar da tsarin kasuwancin Afirka gaba.
Ya lura cewa kamar yadda ƴan kasuwa suka haɓaka kwarin gwiwar gudanar da kasuwanci ta kan iyakoki ba tare da sun haɗu ba, hukumomin tsara dokoki su ma dole ne su faɗaɗa wannan amincewa tsakaninsu.
- BRICS ta ce Bankin NDB zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa
- Dakatar da yaki: Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun goyi bayan BRICS
- Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Bamanga Tukur, ya rasu.
“Ziyarar bincike ta yau ita ce babban matakin farko da muke ɗauka wajen bayyana waccan amincewa. Mun gina tsarin kwakwalwa mai haɗa bayanai (interoperable system) wanda zai iya sadarwa gaba ɗaya, ta yadda ko da ɗan kasuwa daga Najeriya yake dauke da Naira, sannan ɗan kasuwa daga Seme yake ɗauke da Sefa (CFA), tsarin da muke da shi zai haɗa su biyun sannan ya sa kasuwanci ya kasance mai matukar sauƙi,” in ji Adeniyi.
Ya ƙara da cewa samun nasarar haɗa tsarin zai ba ƙasashen biyu damar daidaita sauran manufofin kasuwanci, gami da jerin kayayyakin da aka hana shigo da su, domin samun haɗakar tattalin arziki mai zurfi.
“Idan muka sami nasarar haɗa na’urorinmu daidai, za mu iya gina kowane abu a kan wannan. Za mu iya farawa ta hanyar daidaita jerin kayayyakin da muka hana. Wannan kuma shi ne farkon haɗakar tattalin arziki mai ma’ana tsakanin al’ummominmu.”
Darakta Janar na Hukumar Fito ta Jamhuriyar Benin, Kanal Raouf Aboudou, ya kwatanta CGC Adeniyi a matsayin jagora mai aiki da hankali da gaskiya.
Ya bayyana cewa Shirin Zamantar da Kanikancin Haɗin Gwiwa ya yi daidai da tsarin Haɗin Gwiwa don shawo kan Haɗari (Coordinated Risk Management), wanda yana ɗaya daga cikin manyan ƙa’idodin Ƙungiyar Hukumar Fito ta Duniya (WCO).