Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya gabatar da wasu tsare-tsare guda biyar domin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen BRICS, yayin da China ke shirin karɓar shugabancin ƙungiyar a shekara mai zuwa.

Xi ya gabatar da tsare-tsaren ne a ranar Lahadi, yayin da yake jawabi a zama na biyu na taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 18.

Mafi yawan tsare-tsaren sun mayar da hankali ne kan harkokin ƙirƙirarriyar fasaha (AI) da masana’antar zamani ta dijital da kera kayayyaki ta hanyar fasaha, da bunƙasa ƙwararrun ma’aikatan kimiyya da fasaha.

Xi ya ce China za ta jagoranci ƙoƙarin kafa ƙungiyar buɗaɗɗen tsarin AI ta BRICS, wadda za ta tallafa wa haɗin gwiwar ƙasashe wajen haɓaka da amfani da manyan tsarin harshe na AI.

Ya kuma bayyana cewa China za ta shirya tarurruka na musamman da kwasa-kwasan horaswa kan AI, tare da yin aiki domin samar da wani tsari na AI mai buɗaɗɗen damar amfani.

A wani shiri, China ta gabatar da kafa haɗin gwiwar yankunan tattalin arziki na musamman na BRICS, inda ƙasashe za su iya samar da wata ƙofa ta fasahar zamani, daidaita manufofinsu da kuma ƙirƙirar sabuwar hanya ta bunƙasa tattalin arziki cikin tsari.

Xi ya kuma ce China za ta karɓi bakuncin Taron BRICS kan Kasuwancin Ayyuka a shekara mai zuwa, domin samar da sabbin hanyoyin bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci.

China ta kuma gabatar da shawarar kafa ƙungiyar horas da injiniyoyi ta BRICS, domin ƙasashen ƙungiyar su haɗa kai wajen horas da injiniyoyi tare da amincewa da ƙa’idojin tantance ƙwarewarsu a tsakanin ƙasashe.

Tsare-tsaren na Xi sun nuna yadda China ke ƙara mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da fasaha tsakanin ƙasashen BRICS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *