'Yan wasan Chelsea yayin murnan zura kwallo a ragar Man Utd

Chelsea ta casa Manchester United da ci 5-0 a gasar cin kofin mata ta WSL da suka buga a ranar Asabar.

Wannan sakamakon na nuni ga yadda Chelsea ta farfaɗo sakamakon tashi canjaras da ci 1-1 da Aston Villa a wasan su na farko na gasar ta WSL.

Sjoeke Nüsken, da Keira Walsh, da Lauren James, da Ellie Carpenter da kuma Lucy Bronze duk sun ci kwallaye yayin da Chelsea ta yi wa Manchester United wankin babban bargo.

A halin yanzu, United ta yi rashin nasara a wasanni biyu da ta buga a jere.

A wasanta na farko, ta sha kaye a hannun ƙungiyar London City Lionesses da ci 2-1.

Ƙwallon farko da Chelsea ta ci ya zo ne sakamakon kuskuren da Dominique Janssen, ta yi na kasa cire kwallon da tazo ya na tsalle, lamarin da ya ba Wieke Kaptein damar shiga da sauri ta janye ƙwallon ta baiwa Nüsken wadda ta zura cikin raga da sauƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *