Tawagar haɗin gwiwa tsakanin FIFA da CAF da ke nazarin shirin gyare-gyaren ƙwallon ƙafa na Najeriya zai kammala taron sa a Abuja a ranar Talata, 15 ga Satumba, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafan ƙasar game da makomar hukumar kwallon kafar kasar NFF.
Tawagar ta fara taron ne a ranar Litinin a filin wasa na ƙasa na MKO Abiola dake Abuja, da karfe 11:00 na safe, kuma ta kammala tattaunawarta da misalin karfe 9:35 na dare a Otal din Continental, bayan jerin tarurruka da jami’an gwamnati, masu gudanar da ƙwallon ƙafa da sauran masu ruwa da harkar wanni.
Da isowar su Abuja, tawagar FIFA/CAF ta gana da Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), Mallam Shehu Dikko, a ofishinsa.
-
NPFL: Sporting Lagos ta yi nasara a waje, Barau ta lallasa Ranchers Bees
-
Najeriya ta yi wa New Caledonia wankan tsarki da ci 10-1
-
Najeriya ta miƙa buƙatar karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya ta 2030
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan manufofin da gyare-gyare da aka shirya domin sake fasalin ƙwallon ƙafar Najeriya, bisa tsarin doka da kuma hadin kai tsakanin dukkannin masu ruwa da tsaki.
Dikko ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, FIFA, CAF, Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) da sauran masu ruwa da tsaki wajen gina ingantaccen tsarin ƙwallon ƙafa mai dorewa.
Wakilin FIFA, Rolf Tanner, ya bayyana cewa dalilin zuwan tawagar shi ne sauraron masu ruwa da tsaki, tuntuba da fahimtar taswirar gyare-gyaren da aka gabatar da kuma tantance halin da ake ciki kafin gabatar da rahotonsu ga shugabancin FIFA.
Bayan kammala taron da NSC, tawagar ta tattaunawa da shugabancin NFF da wakilan kungiyoyi mambobin NFF daban-daban, ciki har da Hukumomin Kwallon Kafa na Jihohi, da Hukumomin Shirya Gasa na cikin gida, ‘yan wasa, da masu horarwa da kuma alkalan wasa.
An kuma gayyaci tsoffin shugabannin NFF da sakatarori, mamallaka kungiyoyi, masu daukar nauyi da sauran kwararru a fagen kwallon kafa domin gabatar da ra’ayoyinsu kan gyare-gyaren da aka gabatar.
Tattaunawar za ta ci gaba a ranar Talata, inda ake sa ran tawagar za ta hadu da wakilan Kungiyar Marubutan Wasanni ta Najeriya (SWAN), ciki har da tsoffin shugabanni da sakatarori, da kuma sauran masu ruwa da tsaki da ba su samu damar gabatar da ra’ayoyinsu ba a taron na Litinin.
Ana sa ran sakamakon tattaunawar zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara mataki na gaba da kuma daukar tsarin da ya kamata wajen dawo da kwanciyar hankali kan shugabancin Hukumar NFF da kuma dawo da martabar kasar a harkar wasannin kwallon kafa ciki da wajen kasar.