Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta ce tana ƙoƙarin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da rundunar sojin Indonesia domin inganta ayyukan soji, ƙwarewar jami’ai da kuma ƙarfin hukumomin tsaro.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, lokacin da ya karɓi Ɗan Haɗin Kan Tsaro na Ofishin Jakadancin Indonesia a Najeriya, Kanal Aslam Setiawan, a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
- Saudi Arabia ta ƙi ƙarawa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027
- Ta’aziyyar Bamanga Tukur: Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Yola
- Me ya sa farashin man fetur ke ƙara tashin gwauron Zabi?
Laftanar Janar Waidi ya bayyana dangantakar tsaro tsakanin Najeriya da Indonesia a matsayin wadda ke amfanar ƙasashen biyu, musamman ta fuskar ilimin soji da musayar ƙwarewar gudanar da ayyuka da kuma halartar atisayen soji na ƙasa da ƙasa.
Babban Hafsan Sojin ya kuma yi kira da a faɗaɗa haɗin gwiwar zuwa fannonin yaƙi da tayar da ƙayar baya da sabbin fasahohin zamani da sauran wuraren da ƙasashen biyu ke da muradun soji iri ɗaya.
A nasa jawabin, Kanal Aslam Setiawan ya tabbatar da aniyar Indonesia na ƙara ƙarfafa dangantakar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce musayar ƙwarewa da atisayen soji na ƙasa da ƙasa, na samar da dama wajen inganta haɗin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da Indonesia da musayar ƙwarewar ayyukan soji da kuma ƙarfafa damar rundunonin biyu wajen tunkarar ƙalubalen tsaro na zamani.