Ranar Litinin 21 ga watan Satumba 2026 tashar Blueprint Radio za ta fara watsa shirye-shirye gadan-gadan.
Hukumar gidan rediyon ce ta sanar da haka ranar Alhamis bayan ta samu amincewar Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC).
“Daga ranar Litinin al’ummar Yankin Birnin Tarayya (FCT) za su fara shaida wani kyakkyawan sauyi ta fuskar yada labarai da gabatar da shirye-shiryen rediyo”, inji sanarwar mai dauke da sa-hannun Janar Manajan Blueprint Radio, Muhammad Kabir Muhammad.
Bugu da kari, a cewar sanarwar, “wannan tasha ta Blueprint Radio za ta kawo wa masu sauraro, musamman wadanda aka bar su a baya ta fuskoki daban-daban, bayanan da za su sauya musu rayuwa”.
Sanarwar ta kuma ce tashar za ta fara watsa shirye-shiryen ne bayan ta shafe kusan watanni uku tana watsa shirye-shirye na gwaji, kamar yadda Dokar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa ta tanada.
- JIBWIS ta tattara kusan Naira miliyan 190 daga fatun Layya a 2026
- Kotun ICC ta yi watsi da ƙarar Sunrise kan gwamnatin Najeriya
- Saudi Arabia ta ƙi ƙarawa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027
A cewar sanarwar, Blueprint Radio zai tafi da zamani, ta hanyar wallafa labarai da bayanan da suka shafi al’umma a shafukansa na sadarwa.
Mazauna Yankin Birnin Tarayya za su iya sauraron shirye-shiryen Blueprint Radio kai-tsaye a kan mita 105.3 a zangon FM, yayin da al’umma a sauran sassan Najeriya da ma duniya za su iya sauraro, su ma kai-tsaye, a shafin intanet na www.blueprinthausaradio.com.
Ma’abota shafukan sadarwa na zamani kuwa za su iya samun labarai da bayanai da hotuna da fayafayen bidiyo a Facebook da X da Instagram da TikTok da YouTube idan suka bibiyi @manhajarrayuwa.
Tashar za ta rika watsa shirye-shiryenta ne a harshen Hausa, ganin cewa shi ne harshen da galibin mazauna FCT suka fi amfani da shi.
Tushe daya jaridun Blueprint da Manhaja suke da shi da Blueprint Radio.