Kotu ta bayar da belin Malam Nasir El-Rufa'i [Blueprint]

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a kan kuɗi Naira miliyan 100.

Da take yanke hukuncin, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta gindaya sharadin cewa dole ne wanda zai tsaya wa tsohon gwamnan ya kasance babban ma’aikaci wanda yake kan matakin albashi na 17,  mazaunin Gundumar Maitama ko Asokoro dake Abuja, kuma wanda ya mallaki kadara da ta kai Naira miliyan 100.

Sannan Kotun ta gindaya sharadin cewar dole ne mai neman belin ya gabatar da takardar mallakar fili ko gida wato (C of O) ta asali, ga ofishin Babban Magatakardar Kotun a matsayin ajiya.

Haka zalika, lallai ne wanda zai tsaya neman belin El-Rufa’i ya nuna shaidar karɓar albashinsa na akalla watanni uku na baya-bayan nan, da kuma bayanan hada-hadar kudade da ya yi daga babban manajan bankin da yake hulda da shi.

Jaridar Blueprint ta ruwaito a shafinta na intanet cewar yayin zaman kotun da aka yi a baya, an fuskanci jinkiri wajen amincewa da buƙatun belinsa, inda kotunan ke cewa sai an cika dukkanin ƙa’idodin shari’a kafin sakin sa.

Tsohon Gwamnan na fuskantar zarge-zarge da suka jibanci badaƙalar kuɗaɗe a lokacin da yake gwamna, da kuma laifin bibiyar wayar Mashawarci ga Shugaban Kasa kan Tsaro Malam Nuhu Ribaɗu.

Kawo yanzu, hankula sun karkata ne ga yadda za a cika waɗannan tsauraran sharuɗɗan da kotu ta gindaya, kafin a koma ga ainihin sauraron kararrakin, inda ɓangaren masu ƙara da na kariya suke shirin gabatar da gamsassun hujjojinsu na shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *