Wata ƙungiyar zamantakewa da siyasa na NF ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar Arewacin Najeriya da su mutunta tsarin karɓa-karɓa na mulki, ta hanyar goyon bayan ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake tsayawa takara, domin bai wa Kudancin ƙasar damar kammala wa’adin shekaru takwas na shugabancin ƙasa.

Da yake magana ranar Juma’a a Abuja, yayin ƙaddamar da ƙungiyar a hukumance, ɗaya daga cikin masu haɗa kan shirin kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada cewa adalcin siyasa da zaman lafiyar ƙasa na buƙatar bai wa Kudancin ƙasar dama daidai da Arewa.

Ya ce hana Kudancin ƙasar wa’adi na biyu a jere zai iya kawo cikas ga haɗin kan ƙasa tare da tarwatsa tsarin karɓa-karɓa na shugabancin ƙasa da aka saba da shi.

 

“Kar ku manta, domin a yi adalci, Arewa ta samu nata shekaru takwas ƙarƙashin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma yanzu Kudu ne ke da nata ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu,” in ji Kwamared Waiya. “Don haka bai kamata Arewa ta yi wa Kudu rashin adalci ba. Muna ganin ya kamata mu yi wa ’yan’uwanmu mata da maza na Kudu adalci. Wannan na nufin a bar Kudu ta ci gaba da kammala nata wa’adin, domin daga nan Arewa ta kasance cikin shiri domin sake samun cikakken zagayen shekaru takwas.”

Da yake gargadin kada a yi wa tsarin siyasa katsalandan kafin lokaci, Kwamishinan ya ce: “Katse wannan tsari zai haifar da rashin zaman lafiya a abubuwa da dama tare da jefa abin da muke da shi cikin haɗari.”

Kwamared Waiya, wanda ke jagorantar Nigeria Forward tare da Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh (SAN), ya bukaci ’yan Najeriya su yi wa Shugaba Tinubu hukunci bisa nasarorin zamantakewa, da tattalin arziki da sauye-sauyen tsari da gwamnatinsa ta samu, maimakon su bi kalaman siyasa kawai.

Da yake bayyana wasu manyan sauye-sauye ƙarƙashin ajandar Renewed Hope, Waiya ya danganta da Shugaba Tinubu rawar da ya taka wajen dawo da daidaito, tabbatar da cikakken ’yancin cin gashin kansu na ƙananan hukumomi, da kuma ƙoƙarin samar da tsarin ’yan sandan jihohi domin tunkarar matsalolin tsaron cikin gida.

“Wannan shi ne karo na farko a tarihi da ƙananan hukumomi suka samu cikakken ’yancin cin gashin kansu, kuma mun ga ana raba kuɗaɗen ƙasa ga dukkan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi cikin lokaci,” in ji Waiya, yana ƙara da cewa Jihar Kano ta riga ta kafa kwamitin aiwatar da tsarin ’yan sandan jiha.

Ya gargadi masu sharhi daga Arewa kan su guji hare-haren kafafen yaɗa labarai, yana mai ba da shawarar cewa masu ruwa da tsaki a yankin su riƙa tuntuɓar gwamnati ta hanyar tsare-tsaren ci gaban da aka tsara, maimakon adawa da ta samo asali daga siyasa.

“Ba za mu bari wasu ra’ayoyi da ’yan siyasa suka yaɗa ko suka inganta, waɗanda da gangan aka tsara domin gurɓata tunanin ’yan Najeriya game da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, su rinjaye mu ba,” in ji Waiya. “Ba za mu bari hakan ya ci gaba ba, domin mun yi imanin cewa wa’adinsa ya cancanci a sake ba shi dama.”

Shi ma Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh (SAN), wanda ke haɗa jagorancin ƙungiyar tare da Waiya, ya bayyana Kungiyar a matsayin wata gada ta ƙasa da ke haɗa ’yan ƙasa daga tushe da sakamakon manufofin gwamnatin tarayya da ake iya gani.

Tun da farko, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara, Hon. Mannir Mu’aza Haidara, ya bayyana Kungiyar a matsayin wata kafa da aka samar a kan lokaci daga ’yan Najeriya masu kishin ƙasa domin inganta tattaunawa mai ma’ana, haɗin kan ƙasa da kuma ci gaba mai ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *