Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’ummar Najeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana fara shirye-shiryen Blueprint Radio da cewa babban cigaba ne ga harkar yada labarai a Najeriya.

Ministan ya fadi haka ne a wani sakon fatan alheri da ya aiko wa tashar ta Blueprint a daidai lokacin da take kaddamar da shirye-shorye gadan-gadan ranar Litinin.

“Lallai wannan wani babban cigaba ne ga kamfanin [Blueprint Broadcast Limited], da kuma harkokin yada labaru, da kuma wayar da kan al’ummar Najeriya baki daya,” inji Ministan.

Ministan ya kuma yi kira ga tashar da ta yi aiki bisa ka’ida ta kuma bayar da sahihan labarai.

“Muna kira ga tashar ta tabbatar da ta ba da labaru da shirye-shirye a kan ka’ida domin [amfanin] al’ummar Najeriya baki daya, musamman masu amfani da harshen Hausa a Abuja.

“Allah Ya ba su sa’a, Allah Ya sa abin ya dore, Allah Ya sa albarka a shirye-shiryen nasu,” Inji shi.

Ranar Litinin ne dai tashar ta Blueprint ta fara shirye-shirye gadan-gadan, bayan ta dauki lokaci tana shirye-shirye na gwaji.

Ranar Alhamis din da ta gabata hukumar gidan rediyon ta sanar da haka bayan ta samu amincewar Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC).

“Daga ranar Litinin al’ummar Yankin Birnin Tarayya (FCT) za su fara shaida wani kyakkyawan sauyi ta fuskar yada labarai da gabatar da shirye-shiryen rediyo”, inji sanarwar mai dauke da sa-hannun Janar Manajan Blueprint Radio, Muhammad Kabir Muhammad.

A cewar sanarwar, Blueprint Radio zai tafi da zamani, ta hanyar wallafa labarai da bayanan da suka shafi al’umma a shafukansa na sadarwa.

Mazauna Yankin Birnin Tarayya suna iya sauraron shirye-shiryen Blueprint Radio kai-tsaye a kan mita 105.3 a zangon FM yayin da al’umma a sauran sassan Najeriya da ma duniya za su iya sauraro, su ma kai-tsaye, a shafin intanet na www.blueprinthausaradio.com.

Ma’abota shafukan sadarwa na zamani kuwa za su iya samun labarai da bayanai da hotuna da fayafayen bidiyo a Facebook da X da Instagram da TikTok da YouTube idan suka bibiyi @manhajarrayuwa.

Tashar za ta rika watsa shirye-shiryenta ne a harshen Hausa, ganin cewa shi ne harshen da galibin mazauna FCT suka fi amfani da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *