Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya yi kira ga ƙasashen Global South da su ƙarfafa ƙarfin tattalin arzikinsu na cikin gida, da inganta hukumomi da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen ci gaba mai ɗorewa, yayin da suke fuskantar ƙarin matsin basussuka da sauye-sauye a tsarin ci gaban duniya.
Mahama ya yi wannan kiran ne a wani taron shugabannin ƙasashe da Gidauniyar Open Society ta shirya a birnin New York, a gabanin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
- Najeriya na neman ƙarfafa gargadin bala’o’in yanayi tun kafin su faru
- Ma’aikatan gwamnati sun bai wa Tinubu wa’adin 30 ga Satumba kan tsadar rayuwa
Global South sun ƙunshi ƙasashe masu tasowa da ke fuskantar manyan ƙalubalen tattalin arziki da ci gaba, musamman a Afirka, da Asiya, da Latin Amurka da wasu ƙasashen Caribbean da Pacific.
Daga ƙasashe akwai Najeriya da Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu da Indiya da Indonesia da Brazil da Mexico.
Mahama ya ce ƙasashen na fuskantar ƙarin matsin bashi da kuma sauye-sauye a tsarin tallafin ci gaba na ƙasa da ƙasa, lamarin da ke buƙatar su ƙarfafa hukumominsu da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen ci gaba mai ɗorewa.