Kylian Mbappe da Ousmane Dembele

Kylian Mbappe ya ce babu tashin hankali tsakaninsa da abokin wasansa a tawagar Faransa Ousmane Dembele, bayan maganganun da ya yi cewa shine zai yi nasarar lashe kyautar ta Ballon d’Or.

An zaɓi Dembele a matsayin Gwarzon Ɗan Wasa na Duniya na kakar 2024-25 bayan ya taimaka wa Paris Saint-Germain lashe kambun Gasar Zakarun Turai sau biyu a jere a karon farko.

Dembele, ya zama ɗan wasan Faransa na shida da ya lashe kyautar, inda ya ƙara wa Faransa yawan waɗanda suka lashe gasar tun bayan Zinedine Zidane a 1998.

Mbappe bai taba lashe kyautar ba a duk tsawon rayuwarsa. Matsayi na uku da ya samu a 2023 shi ne mafi girma da ya taba samu a zaɓen na Ballon d’Or.

Yayin da aka tambaye shi ko ya taba tunanin Dembele zai lashe Ballon d’Or kafin shi a wata hira a makon jiya, Mbappe ya ce: “A ko da yaushe ana ganin shi a matsayin kwarren dan wasa. Ni kuma, a koyaushe ana ganina a matsayin zababbe.

Wasu masu sharhi a kafafen yada labarai na Faransa nuna cewa wadannan maganganu ba za su yiwa Dembele dadi ba, yayin da dan wasan gaba na PSG ya mayar da martani da cewa: “Ban taba zama zababbe ba, amma na yi aiki tukuru a bara, inda aka saka mini da sakamako mai kyau a kakan bara tare da PSG.

Duka ‘yan wasan biyu na Les Bleus za su hadu a sansani na farko a ƙarƙashin Zinedine Zidane, yayin da za su kara da Turkiyya a wasan farko na Gasar Nations League na ranar Juma’a, inda Mbappe ya dage cewa babu matsala a tsakaninsu.

Mbappe ya na daya daga cikin manyan ‘yan takarar kyautar Ballon d’Or na bana, duk da cewa bai lashe wani kofi ba a matakin kungiya ko na kasa da kasa a kakar 2025-26.

Mbappe ya ji dadin Gasar Cin Kofin Duniya ta bana, duk da cewa Faransa ta kammala a matsayi na hudu, inda ya karya tarihin zura mafi yawan kwallaye a gasa daya (da kwallaye 10, da kuma taimakawa 4) kuma ya zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar da kwallaye 22.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *