Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce ƙara samun kuɗaɗen ƙananan hukumomi dole ya kasance tare da ƙarin gaskiya da rikon amana, domin jama’a su ga tasirin kuɗin a ayyukan ci gaba.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana hakan a Abuja yayin taron ƙasa na shugabannin ƙananan hukumomi da na majalisun sarakunan gargajiya, inda ya ce yaƙi da cin hanci ba zai tsaya a matakin tarayya ba, sai ya isa matakin da ya fi kusa da jama’a.
- Mutuwar mutane 37 a hannun NSCDC: Gwamnati ta ce ba za ta kare jami’in da aka samu da laifi ba
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya koma NDC
Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda kuɗaɗen da ke zuwa ƙananan hukumomi za su koma ayyuka kamar asibitin matakin farko da ilimi da hanyoyi da ruwan sha da tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa.
Olukoyede ya kuma jaddada cewa babu wani mukami da ya kamata ya sanya mutum ya kasance sama da doka, yayin da ya ce EFCC za ta ci gaba da bincike da gurfanar da masu laifi bisa hujjoji tare da mutunta ikon kotuna.