Kungiyar OK Movement, ta jaddada cewa ita wata ƙungiyar siyasa ce mai cin gashin kanta, kuma ba ta ƙarƙashin tsarin cikin gida na jam’iyyar NDC.
Darakta-Janar na ƙungiyar, John Ughulu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Ughulu ya mayar da martani ne kan kalaman shugaban NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, wanda ya ce ƙungiyoyin tallafa wa ’yan siyasa ya kamata su yi aiki tare da jam’iyyu da tsarin yakin neman zaɓe, maimakon su kafa tsarin da zai iya yin gogayya da jam’iyya.
Sai dai Ughulu ya ce OK Movement ta ƙunshi mutane da mambobin jam’iyyu daban-daban waɗanda suka haɗu wajen goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa Rabiu Kwankwaso.
Ya ce, duk da cewa ƙungiyar tana tallafa wa ’yan takarar NDC, hakan ba ya nufin ta zama reshen jam’iyyar.
Ya ce OK Movement ta gina nata tsarin gudanarwa daga matakin ƙasa zuwa jihohi, ƙananan hukumomi da mazabu, kuma tana da alhakin tafiyar da waɗannan tsare-tsare.
A cewarsa, haɗin gwiwar siyasa tsakanin ƙungiyar da NDC ya kamata a fahimce shi a matsayin haɗin kai wajen cimma manufofin siyasa, ba wai mika ikon gudanar da ƙungiyar ga jam’iyyar ba.
Ughulu ya kuma ce ƙungiyar ba za ta rushe ko haɗewa da NDC ko wata ƙungiya ba.
Ya ƙara da cewa ba za ta mika tsarin da ta kafa a faɗin ƙasar ga wata jam’iyyar siyasa domin gudanarwa ba, sannan za ta ci gaba da tattara magoya baya, yaƙin neman zaɓe da kare kuri’un da aka kada bisa ƙa’ida domin Obi da Kwankwaso.
- Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya samu horon soji — Ministan Tsaro
- NMDPRA ta yi barazanar soke lasisin gidajen mai da ke rage adadin man fetur
Rikicin ya biyo bayan sanarwar OK Movement kan kafa wata majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai mambobi 59.
Sai dai NDC ta nesanta kanta da wannan majalisa, tana mai cewa ba ta samu amincewar kwamitin gudanarwar jam’iyyar ba.
Jam’iyyar ta kuma ce ƙungiyoyin tallafi ba su da ikon kafa tsarin yakin neman zaɓe da sunan NDC ba tare da amincewarta ba.
OK Movement ta ce za ta ci gaba da bin hanyoyin doka da dimokuraɗiyya wajen kare ’yancinta da tsarin da ta kafa.
Ughulu ya ce babu wani mutum da zai iya sanar da rushewa, sauya ko haɗa tsarin ƙungiyar da wata hukuma ba tare da izinin halastattun hukumominta ba, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027.