Rundunar Sojin Mata ta Najeriya (NAWC) ta ce jami’anta sun samu damar gudanar da muhimman ayyukan soji, ciki har da shiga aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Benin.

Kwamandan rundunar mai barin gado, Birgediya Janar Mohammed Adamu, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a lokacin kaddamar da motocin aiki da aka gyara da kuma bude Sabon Kulob din Sojoji da aka gyara na rundunar da ke Giri, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a karon farko Rundunar Sojin Najeriya, ta tura mata sojoji a matsayin cikakkiyar tawaga domin gudanar da aikin tallafa wa zaman lafiya a Jamhuriyar Benin.

Shugaban rundunar Birgediya Janar Mohammed Adamu ya ce an gudanar da aikin ne karkashin Operation ALAFIA, yayin da rundunar ta kuma tura jami’anta zuwa Jihar Plateau karkashin Operation ENDURING PEACE.

A cewarsa, an tura jami’an zuwa Plateau ne domin taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali sakamakon matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Janar Mohammed ya kuma bayyana cewa jami’an Rundunar Sojin Mata sun shiga aikin samar da tsaro yayin zaben gwamnan Jihar Osun da aka kammala gudanarwa.

Ya danganta nasarorin da rundunar ta samu da amincewa, jagoranci da kuma kyakkyawan yanayin aiki da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya samar.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da taimaka wa Rundunar Sojin Najeriya wajen tunkarar kalubalen tsaro na zamani da kuma cika nauyin da aka dora mata na gudanar da ayyukan soji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *