Hukumar Kula da Harkokin rarraba Man Fetur a kan tudu da ruwa ta Najeriya (NMDPRA) ta yi barazanar soke lasisin gidajen mai da aka samu suna rage adadin man fetur da suke bai wa masu saye.
Hukumar ta bayar da umarnin ne cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, bayan rahotannin samun gidajen mai da ke rage adadin man fetur da suke zubawa ga abokan ciniki, a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gab da tashi.
NMDPRA ta bayyana wannan dabi’a a matsayin babban take hakkin amincewar masu amfani da kayayyaki, inda ta umarci masu gidajen sayar da man fetur a fadin Najeriya da su gaggauta daidaita tare da tantance na’urorin awo da na’urorin tantance jimillar man da suke sayarwa.
- Ministan tsaro ya jaddada kudirin Najeriya na wanzar da zaman lafiya a duniya
- Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ranar Alhamis
- Katsina ta cika shekaru 39 da kafuwa
Hukumar ta ce matakin na nufin tabbatar da cewa ana auna man fetur yadda ya kamata, tare da kare masu saye daga karbar man da bai kai adadin da suka biya ba.
NMDPRA ta ce ta kara tsaurara bincike da matakan tabbatar da bin ka’idoji a fadin kasar.
Ta ce gidajen mai da aka samu suna rage adadin man da suke zubawa,da amfani da na’urorin awo da ba a daidaita su yadda ya kamata ba, ko kuma yin duk wani abu da zai kawo cikas ga daidaiton awo, za a bukaci su dauki matakin gyara nan take.
Hukumar ta kara da cewa masu maimaita laifin ko wadanda aka samu da manyan laifuka za su fuskanci hukunci, wanda zai iya kaiwa ga soke lasisin tashar sayar da man, bisa ka’idojin NMDPRA.