Manoma a Jihar Edo sun ce sun fara komawa gonakinsu da ke fadin kananan hukumomi 18 na jihar, sakamakon ingantuwar matakan tsaro da gwamnatin Monday Okpebholo ta dauka.
Shugaban Kungiyar manoma reshen jihar IFAN kuma Shugaban kungiyar All Farmers Association of Nigeria (AFAN), Alhaji Bako Dogwo, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Benin.
- NSCDC ta sake jaddada gaskiya da bin doka yayin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinai
- Dole a ga tasirin kuɗin ƙananan hukumomi a rayuwar jama’a –EFCC
- TCN ta ƙaddamar da sabon tsarin yaƙi da cin hanci
Dogwo ya bayyana hakan ne lokacin da manoman da ke karkashin kungiyoyin IFAN, AFAN da kuma Federated FADAMA Farmers na jihar suka nada Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Edo, Mista Jarrett Tenebe, a matsayin uban girmamawa na manoman jihar.
Ya yabawa Gwamna Okpebholo kan kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta tsaro a fadin jihar, yana mai cewa hakan ya kara wa manoma kwarin gwiwar komawa gonakinsu.
Dogwo ya ce ingantuwar tsaro zai taimaka wajen kara yawan noman abinci da kuma karfafa samar da isasshen abinci a jihar.