Tsohon Shugaban Kasa Goodluck JonathanTsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki da su daina yi wa dimokuradiyya da tattalin arziki kallo na daban.

Dokta Jonathan ya kuma ce dole ne a hada abubuwan biyu waje guda domin samar wa ‘yan kasa rayuwa mai inganci.

Tsohon Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani rahoton bincike na musamman mai taken “Dimokuradiyya ce Ginshiƙin Bunƙasar Tattalin Arziƙi”, wanda gidauniyarsa ta shirya a Abuja.

A  jawabin nasa, wanda aka raba wa manema labarai, Dokta Jonathan  ya jaddada cewa sakamakon binciken ya nuna buƙatar samar da sauye-sauye a hukumomin kasar nan.

“Hanyar da muke bi a yanzu ba mai ɗorewa ba ce, dole ne dimokuradiyya da tattalin arziƙi su kasance masu karfafar juna,” inji shi.

Ya kara da cewa, dimokuradiyya mai karfi ce take samar da yanayin da tattalin arziki zai bunƙasa, sannan idan aka samu bunkasar tattalin arziki dimukradiyya za ta dore.

Wannan sabon rahoto da aka kaddamar ya mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da tsarin mulki wajen taɓa rayuwar talaka, ta hanyar inganta harkar kudi da kasuwanci. Dr. Jonathan ya bayyana cewa wannan shi ne hangen nesa da ya kamata kasar ta sanya a gaba a wannan lokaci.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, wakilan kasashen waje, da masana tattalin arziki.

A halin yanzu, masana na kallon wannan kiran na Dr. Jonathan a matsayin wani babban darasi ga kasashen Afirka masu tasowa, inda akasari ake samun gibin alaƙa tsakanin tsarin siyasa da jin daɗin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *