A wani mataki da ya girgiza masu neman takardar izinin tafiya ƙasashen waje, Ofishin Jakadancin Amurka dake Abuja ya sanar da dakatar da dukkan ayyukan bayar da visa har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba.

Ofishin ya bukaci dukkan masu nema da su duba akwatunan sakonninsu na email domin samun cikakken bayani kan yadda za a sake tsara musu wani lokacin.

Sai dai sanarwar ta ce ayyukan visa a Ofishin Jakadancin Amurkan dake Legas ba su dakata ba.

Ta kuma ce ana ci gaba da ayyukan gaggawa don ‘yan ƙasar Amurka dake Najeriya ta hanyar wani tsari na musamman.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bayar da umarnin janye ma’aikatan Ofishin, sakamakon fargabar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya.

Wannan mataki zai shafi dubban mutane da ke shirin tafiya karatu ko kasuwanci ko ziyara zuwa Amurka.

Da take mayar da martani, gwamnatin Najeriya ta soki matakin da ƙasar Amurkan ta ɗauka. Sannan tace ba bu ƙamshin gaskiya game rashin a tsaro a Abuja.

Gwamnatin Najeriyar tace sanarwar ka iya sanya fargaba maras dalili ga mazauna Abuja da kuma masu zuba jari.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa wannan mataki zai iya ƙara takura wa alaƙar da ke tsakanin kasashen biyu, musamman ta fuskar diflomasiyya da sufuri.

Da safiyar ranar Alhamis ne wata sanarwa daga Shugaban na Amurka ta bukaci ma’aikatan da ba na musamman ba su koma gida sakamakon matsalar tsaro a sassan arewacin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *