Shin Sadiya Umar Farouq za ta mika kanta? Mai sharia Omotosho yace sun daina lallashi ta bayyana a gabansu domin amsa tambayoyi

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da takardar sammacin kamo tsohuwar Ministar Jinkai da Cigaban Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Faruq, da karfin tuwo.

Umarnin ya biyo bayan bukatar da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta gabatar, sakamakon gazawar tsohuwar Ministar ta amsa gayyatar da aka sha yi mata domin kare kanta a baya.

Bayan gamsuwa da bayanan masu shigar da kara, wato EFCC, cewa tsohuwar Ministar ta ki bayyana a gabanta sau da dama ba tare da wani kwararan dalili na shari’a ba, hakan ya sanya Mai sharia James Omotosho yin amfani da karfin iko domin kamo ta.

Ana binciken Sadiya Umar Farouq ne kan zargin karkatar da kudaden ayyukan jin kai da suka shallake sama da naira biliyan 37, da ake zargin an rarrabasu  ta wasu kamfanoni da ke da alaka da wasu manyan jami’an gwamnati.

Wannan mataki na daya daga cikin gagarumin binciken da gwamnatin shugaba Tinubu ke gudanarwa a ma’aikatar jin kai, inda tuni aka dakatar da wasun su.

Alkali Omotosho ya jaddada cewa dokar kasa ta fi karfin kowa, kuma dole ne wanda ake zargi ya bayyana domin bincike ya kammala. Umarnin kotun ya ba wa jami’an EFCC damar kamo tsohuwar ministar a duk inda take a fadin Najeriya domin ta fuskanci tambayoyi.

A halin yanzu, ‘yan Najeriya na zura ido su gani ko tsohuwar ministar za ta mika kanta ko kuma jami’an hukumar za su yi amfani da sabon ikon da suke dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *