Mijin Shugabar ƙasar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, Hafidh Ameir Hassan, ya rasu a wani asibiti da ke Zanzibar babban birnin kasar, bayan fama da rashin lafiya.
Mataimakin Shugaban ƙasar, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar Hafidh Ameir, inda ya bayyana cewa marigayin ya kasance yana fama da ciwon zuciya.
Ndejembi ya ƙara da cewa an fara shirye-shiryen jana’izarsa a tsibirin Kizimkazi, da ke kudu maso yammacin Zanzibar.
- An yanke wa wata fitacciyar ‘Yar Jarida hukuncin rataya
- Iran ta kai hari kan wani jirgin ruwa mara matuki na sojin Amurka a Mashigar Hormuz
- Aƙalla Mutane 25 sun mutu a hatsarin bas a Cape Verde
Hafidh Ameir malami ne a fannin noma, kuma ya kasance mutum mai ƙarancin bayyana kansa a bainar jama’a,
inda ya zama Mijin shugabar kasa na farko a Tanzaniya bayan hawa mulkin Samia Hassan a shekarar 2021.
Ya auri Samia Hassan a shekarar 1978, kafin ta shiga siyasa, sun haifi ‘ya’ya huɗu da suka hada da maza uku da mace ɗaya.
‘Yarsu, Wanu Hafidh Ameir, ita ma ‘yar siyasa ce, kuma a halin yanzu tana wakiltar Zanzibar a Majalisar Wakilai ta ƙasar Tanzaniya.