Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamna Abba Yusuf da ya gaggauta ɗaukar matakan dakile barkewar cutar gudawa, wadda rahotanni suka ce ta yi sanadin mutuwar sama da yara 50 a ƙaramar hukumar Rano.
Kiran ya biyo bayan wani ƙuduri na gaggawa kan al’amuran da suka shafi jama’a, wanda ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Litinin, wanda Kakakin Majalisar, Ismail Falgore, ya jagoranta.
- Tagomashin da Najeriya ke samu daga cire harajin fiton kaya daga Chaina
- Goodluck Jonathan, ya nuna damuwarsa kan ƙarancin jami’o’in Afirka a cikin jerin manyan jami’o’i 100 na farko
- 2027: Obi ya saba wa Atiku, ya goyi bayan janye tallafin mai
Yayin gabatar da ƙudurin, Muhammad ya ce barkewar cutar ta fi tsanani a yankunan Rurum da Sabuwar Ƙaura na ƙaramar hukumar, inda ta yi sanadin mutuwar sama da yara 50.
Ya ce: “Ko da yake an ɗauki matakan gaggawa, ciki har da sayen magunguna da tura ma’aikatan lafiya zuwa al’ummomin da abin ya shafa, har yanzu ana buƙatar ƙarin shiga tsakani domin shawo kan barkewar cutar.”
Muhammad ya buƙaci Gwamna Yusuf da Kwamishinan Lafiya na jihar su samar da ƙarin tallafin gaggawa ga al’ummomin da cutar ta shafa.