“PDP ta mutu” – wannan ne abin da Shugaban Majalisar Datatwa Godswill Akpabio ya furta lokacin da yake karanta wasikun da wasu sanatoci suka rubuta wa Shugabancin Majalisa suna sanar da sauya shekarsu daga wasu jam’iyyu zuwa wasu wasu.
Ranar Alhamis ne dai sanatocin su tara suka mika takardun sanar da ficewarsu daga jam’iyyu daban-daban zuwa ADC – jam’iyyar da wasu jiga-jigan ’yan adawa suka shiga inuwarta don yakar APC a zaben badi.
Daga cikin sanatocin biyar ’yan PDP ne, daya ’yar LP, daya kuma dan YPP.
Akwai mutum biyu da ba a tabbatar da sauya shekar ba.
A farkon wannan wannan wata na Maris dai, PDP na da sanatoci 17 ne.
Sai dai bayan sauya shekar wasu daga cikin sanatocin a ranar Alhamis, da kuma wasu uku da suka bar ta ranar 11 ga watan Maris, yanzu haka sanatoci takwas suka rage mata.
Rikicin cikin gida
Daya daga cikin dalilan da wadannan ‘’yan majalisa suka bayar na sauya sheka shi ne rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa a jam’iyyar ta PDP.
Idan ba a manta ba, tun bayan Manyan Zabubbukan 2023 PDP take fama da rikicin shugabanci.
A yunukrinta na shawo kan wannan matsala ta shirya Babban Taro na Kasa a ranakun 15 zuwa 16 na watan Nuwamban bara a birnin Badun.
Sai dai kuma wasu shugabannin jam’iyyar sun sanar da korar shugabanninta sannan suka nemi kotu ta hana yin taron.
Daga bisani shugabannin na PDP suka samo hukunci daga Babbar Kotun Jihar Oyo da ya bas u damar gudanar da taron.
A wajen taron aka sanar da korar shugabannin bangaren da ya nemi kotu ta haramta shi, da ma Ministan Yankin Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike, wanda ake zargi da goya musu baya.
Alkawari Kabiru Turaki
Sai dai kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ba ta halarci wajen taron ba, balle ta sa ido a kan yadda ya gudana.
Wannan ya sa wasu suke ganin duk wata shawara da aka yanke a lokacin ba ta da wani tasiri, ciki har da korar su Wike da ma zaben Barista Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon Shugaban Jam’iyya na Kasa.
Amma dai cike da kwarin gwiwa, Kabiru Turaki ya sa kafa ya shure wannan ra’ayi yana mai cewa tun da sun sanar da INEC a kan lokaci kamar yadda Doka ta tanada, to Rashin zuwan hukumar zabe ba matsalarsu ba ce.
Ya kuma lashi takobin ganin ya hada kan ’ya’yan jam’iyyar ta yadda za su farfado da ita kafin Zabubbukan 2027.
Wankin hula
Sai dai kuma ga alama wankin hula yana nema ya kai su dare.
Kokarin da Shugabancin PDP bangaren Kabiru Tanimu Turaki ya yi don ganin ya sama wa kansa halalci ma ya ci tura.
Awaki lokacin da ya garzaya kotu yana neman ta tilasta wa INEC amincewa da shugabancin, amma kotun ta ce Shugabancin bai halalta ba, saboda hukumar ba ta shaida zabensa ba.
A Majalisar Dattawa
Kasancewar sanatoci tara da suka sauya sheka a baya-bayan nan ADC suka koma, yanzu jam’iyyar ta yi wa PDP kafara baya, a karon farko ta zama ta biyu wajen yawan mambobi a Majalisar ta Dattawa.
Ficewar Aminu Waziri Tambuwal da Mohammed Ogoshi Onawo ba karamar asara ba ce ga PDP saboda tasirinsu a majalisar.
Sannan kuma APC ta zama gagarabadau a majalisar, lamarin da ka iya raunanan matsayin jam’iyyun adawa.
Hakan na nufin APC za ta ci karenta babu babbaka a Majalisar.
Sanatocin da suka sauya sheka
– Aminu Waziri Tambuwal (Kudancin Soakkwato) – PDP
– Mohammed Ogoshi Onawo (Kudancin Nasarawa) – PDP
– Binos Dauda Yaroe (Kudancin Adamawa) – PDP
– Austin Akobundu (Tsakiyar Abiya) – PDP
– Lawal Adamu Usman (Kaduna ta Tsakiya) – PDP
– Ireti Kingibe (FCT) – LP
– Enyinnaya Abaribe (Kudancin Abiya) – YPP
– Wasu biyu da ba a tabbatar ba tukunna