'Yan wasannin Barau FC yayin murnar doke Abia Warriors

Ƙungiyar Barau FC ta ci gaba da samun nasara a Gasar Firimiyar Najeriya ta NPFL bayan doke Abia Warriors da ci 2-0 a wasan mako na biyar da suka buga a garin Kano, ranar Laraba, 23 ga watan Satumbar 2026.

Har yanzu babu wata ƙungiya da ta doke Barau FC a kakar wasan bana cikin wasanni biyar da ta buga, inda ta ke jan ragamar teburin Gasar NPFL da maki 11.

Ƙwallayen da Joseph Atule da kuma Ibrahim Ayoola suka ci, su suka tabbatarwa Barau FC da nasara yayin fafatawar.

A wani wasan na daban, Sporting Lagos ta samu gagarumar nasara, inda ta je gidan Enyimba FC kuma ta doke ta da ci 3-2 a wasa mai ban sha’awa da ƙayatarwa wanda suka buga a ranar Laraba.

Rangers ta sha da ƙyar da ci 1-0 a hannun Ranchers Bees, yayin da Doma United da Plateau United suka raba maki a wasan da suka tashi ci 2-2.

Bendel Insurance ma ta samu maki uku bayan ta lallasa Ikorodu City da ci 2-1.

Ga Sakamakon Wasannin NPFL Na Mako Na Biyar Da Aka Buga

Rangers 1-0 Ranchers

Barau FC 2-0 Abia Warriors

Enyimba FC 2-3 Sporting Lagos

Bendel Insurance 2-1 Ikorodu City

Shooting Stars 2-0 Katsina United

Kwara United 2-1 Nasarawa United

Inter Lagos 1-1 Kano Pillars

Niger Tornadoes 0-0 Warri Wolves

Doma United 2-2 Plateau United

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *