Mahajjata akalla miliyan 1.8 ne suka tsaya a filin Arfa da ke da nisan kilomita 20 daga birnin Makka na kasar Saudi Arabia ranar Talata.
Yayin tsayuwar, mahajjatan sun yi ta kabbarori da hailala da tahmidi da karatun Alkur’ani da addu’o’in neman gafarar Ubangiji.
Sun kuma saurari huduba daga Limamin Masallacin Manzon Allah Shaikh Ali Bin Abdurrahman Huzaifi, wanda ya jaddada Tauhidi a matsayin daya daga cikin shikashikan Musulunci.
- Tashar Blueprint Radio ta fara shirye-shiryen gwaji
- Kotu: Jonathan na da Ikon tsayawa takarar Shugaban ƙasa
- Sheikh Gumi ya zargi wasu kafafen yada labarai da sauya masa zance
Daga nan ne kuma Sheikh Ali ya jagoranci sallolin Azahar da La’asar, sannan mahajjatan suka zauna zuwa faduwar rana lokacin da za su yi tattaki zuwa Muzdalifa don jifan Shaidan.
Tun ranar Litinin mahajjatan, gaba dayansu sanye da farin ihrami, suka hallara a Mina don fara aikin Hajjin bana.
Bayan sallar Asuba ne mahajjatan suka dunguma suka nufi Filin Arfa don yin aiki mafi girman lada a aikace-aikacen Hajji.
Malamai sun ambato Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabata a gare shi yana cewa, “Tsayuwar Arfa ce Hajji”.
Ranar Arfa, wato 9 ga watan Zul Hijjah, ita ce rana mafi muhimmanci a kalandar Addinin Muslunci.
Malaman Musulunci sun ce ranar tana cike da rahama da gafara da albarka.
Ita kuma ce kuma ta dace da ranar da Manzon Allah (SAW) ya yi hudubarsa ta karshe, wadda a ciki ya yi gamsasshen bayani game da adalci da mutunta dan’Adam da daidaito a tsakanin mutane da ma kyakkyawar mu’amala da zamantakewa.
Rahotanni sun ambato hukumomin Saudiyya suna cewa mutanen da aka yiwa rajista sama da miliyan daya da rabi ne suka shiga kasar daga waje don gudanar da aikin Hajjin na bana.
