‘Yan wasa da jami’an ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crown FC dake garin Ogbomoso, sun yi mummunan hatsarin mota a ranar Alhamis yayin da suke kan hanyar su ta zuwa Ijebu Ode, jihar Ogun, domin halartar gasar cin kofin share-fage ta AFH.
An rahoto cewa motar ƙungiyar ƙirar Toyota Coaster ta yi karo da wata babban mota (tirela) a yayin da tawagar ke kan hanyarsu ta zuwa filin wasa na Ebedei, wanda shi ne filin da za a gudanar da gasar.
Hatsarin ya yi sanadin jikkata direban motan sosai, yayin da wasu daga cikin ‘yan wasa da jami’ai ma suka samu raunuka kuma aka garzaya da su domin samun kulawar likita.
Sai dai daga baya jaridar Blueprint.ng ta gano cewa direban motar ya mutu sakamakon raunin da ya samu. Ba a samu cikakkun bayanai nan take ba game da yadda hatsarin ya faru ko kuma halin da ‘yan wasa da jami’an da suka ji rauni ke ciki.
-
Mustapha Abdullahi ya yi alƙawarin kawo gyare-gyare da cigaban wasan ƙwallon kwando a Najeriya
-
Kyaftin din Najeriya Rasheedat Ajibade za ta yi jinya tsawon lokaci sakamakon raunin da ta ji a kafarta
-
Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata U17: Flamingos na fatan samun nasara a kan Poland
A wata sanarwa ta farko da Crown FC ta fitar bayan hatsarin, ta tabbatar da cewa direban ya samu mummunan rauni, sannan wasu mambobin tawagar ma sun ji rauni.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ana ƙoƙarin ganin cewa duk wanda abin ya shafa sun samu kulawar likita ta gaggawa.
“Kungiyar tana so ta tabbatar wa kowa cewa duk ‘yan wasa da jami’an da suka jikkata an garzaya da su zuwa asibiti dake kusa domin samun kulawar likita nan take. Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan sanarwa, ba a kai ga samun rahoton mutuwar wani ba,” inji sanarwar.
Da farko dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa babu wanda ya mutu a lokacin da ta fitar da sanarwar. Sai dai bayanan da jaridar Blueprint.ng ta sake tattarawa daga baya sun nuna cewa daga bisani direban ya mutu sakamakon raunin da ya ji.
Hukumar gudanarwar ta bayyana damuwarta kan lafiyar ‘yan wasa da jami’an, inda ta tabbatar wa magoya baya da masu ruwa da tsaki cewa ana daukar matakan da suka dace domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
Haka zalika, kungiyar ta yi kira ga jama’a da su guji yada kalaman da ba su da tabbas game da lamarin, yayin da take godiya ga magoya baya da masu ruwa da tsaki kan damuwar da suka nuna da kuma goyon bayan da suke ba su.
Ba a samu cikakkun bayanai nan take ba game da adadin ‘yan wasa da jami’an da suka ji rauni, da halin da suke ciki a yanzu, ko kuma yadda hatsarin ya faru a lokacin da ake fitar da wannan rahoton.
