An cire tawagar ‘yan wasan Golden Eaglets ta Najeriya daga gasar ‘yan kasa da shekaru 17 ta WAFU B bayan sun tashi 1-1 da Young Elephants ta kasar Ivory Coast a ranar Asabar, a wasan karshe na rukuni da suka buga a filin wasa na Stade du 4 Août da ke birnin Ouagadougou.
Najeriya ta farfado daga baya inda ta rama kwallon da aka zura mata a minti na 84 ta hannun Abiodun John.
Alex Fousseni ne ya fara zura wa Eaglets kwallo a ragar ta a minti na 16 da fara wasa.
-
An tabbatar da mutuwar direban kungiyar Crown FC, yayin da ‘yan wasa da jami’ai suka jikkata a wani hatsarin mota
-
Kyaftin din Najeriya Rasheedat Ajibade za ta yi jinya tsawon lokaci sakamakon raunin da ta ji a kafarta
-
Mustapha Abdullahi ya yi alƙawarin kawo gyare-gyare da cigaban wasan ƙwallon kwando a Najeriya
A baya dai Eaglets din ta sha kaye a wasanta na farko da ci 2-1 a hannun Jamhuriyar Nijar.
Wannan na nufin cewa Najeriya za ta rasa gurbin shiga Gasar Cin Kofin Afrika ta U-17 sau uku a jere, da kuma gasar cin kofin duniya ta U-17 ta FIFA sau hudu a jere.
Lokaci na karshe da Najeriya ta buga Gasar Cin Kofin Duniya ta U-17 ta FIFA shi ne a shekarar 2019.