Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya ce hukumomin tsaro na iya gano maboyar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane idan har suna da niyyar yin hakan.
Yayin wata hira da gidan Talabijin na TVC, Buratai ya ce bai yarda da ikirarin cewa jami’an tsaro ba za su iya gano masu laifin da ke yada bidiyoyinsu da sakonninsu daga maboyarsu ta hanyar kafafen sada zumunta ba.
Ya ce idan hukumomin tsaro na iya gano mutane masu tasiri a kafafen sada zumunta, babu dalilin da zai hana su gano ‘yan bindigar da ke nuna ayyukansu da dukiyar da suka kwace a fili ba.
Sai dai ya kara da cewa yana ganin hukumomin tsaron na da wasu dalilai, da basa son bayyana wa jama’a komai.
Tsohon hafsan sojin ya kuma yi kira da a kara karfafa hukumomin tsaro ta hanyar daukar karin jami’ai, da horas da su akai-akai, tare da inganta walwalarsu.
“Najeriya na bukatar karin sojoji da ‘yan sanda domin magance matsalolin tsaro da ke kara yawaita a sassan kasar nan.” Inji Buratai
Tsohon Hafsan, ya kuma bayyana cewa rundunar sojin Najeriya na da kwararrun rundunoni na musamman da aka horar domin gudanar da ayyukan ceto mutane da aka yi garkuwa da su.
Ya yi fatan fadada cibiyar yaki da ta’addanci, da kafa rassanta a jihohi, samar da kayan aiki na zamani da kuma hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane.
