Wani kwamitin bincike ya gano cewa hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) ta tsare wani mutum mai suna Emmanuel Emeka kan wata takaddama ta bashin kuɗi da ba ta da alaƙa da haƙar ma’adinai, kafin ya mutu a hannun hukumar a Minna, Jihar Neja.

Rahoton ya bayyana cewa an tsare Emeka ne a lokacin da hukumar ke gudanar da samamen da ya shafi zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ranar 15 da 16 ga Satumbar 2026.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS, ya ce tsare mutumin ya saɓa wa ƙa’idojin doka, kuma an ci gaba da tsare har zuwa lokacin da ya mutu tare da sauran fursunonin.

Binciken ya kuma gano cewa jami’an hukumar sun tsare mutane fiye da lokacin da doka ta amince da shi, tare da kasa tabbatar da ingantattun matakan kare haƙƙin waɗanda ke hannunsu.

Rahoton ya bayyana tsare Emeka a matsayin ɗaya daga cikin misalan gazawar jami’an wajen bin doka da kula da fursunoni, tare da ba da shawarar ɗaukar matakan ladabtarwa da bincike kan jami’an da ke da alhaki.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *