Majalisar Wakilan Najeriya ta ɗage komawa zamanta daga ranar Talata, 10 ga Nuwamba, zuwa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026.
Magatakardar majalisar, Ibrahim Sidi, ne ya sanar da sauyin jadawalin bisa umarnin Kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, inda ya ce wasu muhimman al’amuran ƙasa da ke buƙatar kulawar shugabannin majalisar ne suka jawo dagewar.
- An dawo da ‘yan Najeriya 175 gida daga Libya
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu, sun kuɓutar da mutane uku a Adamawa
A makon da ya gabata ne majalisar ta sanar da cewa za ta koma zaman majalisa a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, kafin daga bisani ta sauya ranar.
Shugabancin majalisar ya nuna nadama kan duk wata matsala da sauyin jadawalin zai iya haifar wa ’yan majalisar.
Ya kuma buƙaci ’yan majalisar da su koma gudanar da ayyukan dokoki a ranar Laraba, kamar yadda aka tsara.