An hana ‘yan wasan Super Eagles nasara mai muhimmanci a daren Laraba bayan Poland ta zura kwallo daf da lokacin tashi, inda aka karkare wasan ci 2-2, a wasan sada zumunta na kasa-da-kasa da suka buga a Warsaw.

Najeriya ce ta fara zura kwallo a ragar Poland a minti na 23 ta hannun Terem Moffi, sannan masu masaukin baki suka rama ta hannun Kacper Potuski, a minti na 45.

Najeriya ta sake yin gaba bayan Paul Onuachu ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 76.

Sai dai Poland ta sake dawowa ta hannun Przemyslaw Wiśniewski da kwallo mai kyau da ya zura a cikin karin lokaci.

Sakamakon wasan ya zama wani muhimmin mataki a shirye-shiryen Super Eagles na wasannin kasa da kasa da ke tafe, tare da shirin kece raini da kasar Portugal a ranar 10 ga watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *