Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a samar da cikakken tsari domin bunƙasa wasanni tun daga matakin ƙananan hukumomi, yana mai cewa dole ne Najeriya ta wuce matakin tattaunawa zuwa ɗaukar matakan da za a iya aunawa, waɗanda za su sauya makomar wasanni a ƙasar.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis, yayin da yake buɗe taron ƙasa kan bunƙasa wasanni daga tushe na shekarar 2026, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, CON, ne ya wakilce shi. Tinubu ya ce matsalar Najeriya ba ƙarancin ƙwararrun ‘yan wasa ba ce, illa rashin isassun tsare-tsare, wuraren wasanni da kuma damar gano matasa masu hazaka da horar da su.
-
Real Madrid ta sanya Yuro miliyan 150 kan Vinícius
-
FIFA ta nada mambobi biyar a kwamitin rikon kwarya na NFF
-
Manchester United ta sallami Michael Carrick daga aikin kocin tawagarta
Ya ƙalubalanci mahalarta taron da su tabbatar da cewa taron na kwanaki biyu ya samar da shawarwari masu amfani, alkawuran da za a iya tantancewa da kuma cikakken tsarin ƙasa da za a iya aiwatarwa.
Shugaban ya bayyana muhimman abubuwa takwas da ya kamata a ba fifiko. Waɗannan sun haɗa da samar da shirye-shiryen wasanni masu ɗorewa a faɗin ƙasar, da gyaran wuraren wasanni na al’umma, da gano ‘yan wasa masu hazaka a matakin ƙasa, da inganta kuɗaɗen tallafi, da bunƙasa ƙwarewar masu horaswa, haɗa wasanni cikin tsarin makarantu, tabbatar da bai wa kowa dama da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci a fannin wasanni.
Ya jaddada cewa bunƙasa wasanni daga tushe dole ne ya zama babban abin da ƙasa ke ba muhimmanci, inda gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi, cibiyoyin ilimi, ƙungiyoyin wasanni da kamfanoni masu zaman kansu za su haɗa kai.
Tinubu ya kuma bayyana wasanni a matsayin wata dama ta tattalin arziki da za ta iya samar da ayyukan yi a fannoni kamar horas da ‘yan wasa, kimiyyar wasanni, kula da wuraren wasanni, aikin jarida, yawon buɗe ido da sauran sana’o’in da ke da alaƙa da su.
Ya buƙaci masu zuba jari a kamfanoni masu zaman kansu da su ɗauki wasanni daga tushe a matsayin fannin da zai iya samar da riba, ba wai kawai abin shakatawa ba.
Haka kuma, shugaban ya yi kira da a ƙara samar da damammaki ga ‘yan mata, da masu bukata ta musamman, da yara daga al’ummomin da ba sa samun isasshen kulawa. Ya jaddada cewa talauci ko wurin da mutum ya fito bai kamata su zama dalilin hana ‘yan Najeriya masu hazaka cimma burinsu ba.
Yayin da yake yabawa waɗanda suka shirya taron bisa haɗa masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-daban, Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar hukumomi da kuma ci gaba da zuba jari a fannin.
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan bunƙasa wasanni daga tushe, Hon. Adeyinka Anthony Adeboye, ne ya shirya taron, tare da tallafin fasaha daga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Najeriya (NESG).
A ƙarshe, shugaban ya ayyana buɗe taron a hukumance, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa tattaunawar za ta samar da sakamako mai ɗorewa domin amfanin al’ummomin da za su zo nan gaba.
