Sabon ɗakin karatun yana da kujerun zama guda 1,000, tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin kilowatt 30, ɗakin kallon shirye-shiryen bidiyo da labarai, da sauran sassan karatu na zamani.
- NDLEA ta ƙwato abubuwan fashewa 160 da miyagun ƙwayoyi a jihohi daban-daban
- Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum bakwai a Neja
An gina ɗakin karatun ne domin bai wa ɗaliban da ke karatun digiri na farko da na gaba damar samun ingantaccen yanayin karatu da bincike.
Bayan ƙaddamar da sabon ginin, za a mayar da tsohon ɗakin karatun kwalejin cibiyar karatu ta intanet, wato e-library, domin gudanar da bincike ta hanyar fasahar zamani.
Rundunar ’yan sandan ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na samar wa ɗaliban kwalejin kayan karatu na zamani, domin su samu ilimi da ƙwarewar da za su ba su damar yin gogayya da takwarorinsu a manyan jami’o’in Najeriya.