Gamayyar kungiyoyin kare ‘yancin mata sun bukaci jam’iyyu su barwa Mata matsayin mataimakan gwamna a jihohi 36, a gwamnati mai kamawa.

Yayin taron manema labarai a ranar Laraba, Babbar Daraktar Gudanarwa ta gamayyar kungiyoyin (Voice of Women Empowerment Foundation), Misis Toun Okewale Sonaiya, tace  mata na fuskantar tursasawa tun daga zaben fidda gwani.

Sonaiya ta nanata cewa duk da cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya tanada, cire mata daga shugabanci yana haifar da rikicin siyasa da kuma koma baya ga dimokradiyya.

Sonaiya ta koka da cewa duk da cewa mata sun kai kusan rabin al’ummar Najeriya, amma har yanzu ba a ba su isasshen gurbi a Wakilci da Shugabanci.

“Ga kowane dan takarar gwamna namiji, dole ne jam’iyyun siyasa su gabatar da mace a matsayin mataimakiya, hakan ka iya samar wa mata damar zama gwamnoni a nan gaba”, in ji sonaiya.

Daraktar ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu, ya yi amfani da tasirinsa wajen ganin an zartar da kudirin dokar samar da kujeru na musamman da aka warewa mata, da ke gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *