Mahara dauke da makamai sun sace mutum hudu tare da kashe dan banga daya a wani hari da suka kai yankin Byazhin da ke Kubwa, Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana kansa da suna Aliyu, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis.

“‘Yan bindigar da yawan su ya kai kusan 28 da sun kai hari yankin. Ina tsammani sun tafi da mutum hudu cikin daji yayin da aka harbi dan banga daya da ke tsaron yankin daga baya kuma ya mutu,” in ji Aliyu.

Majiyar jami’an tsaro, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an riga da an binne dan bangar da aka kashe.

Majiyar ta kuma bayyana cewa hadakar jami’an tsaro sun kaddamar da aikin bincike don ceto wadanda aka sace.

“Gaskiya ne. An riga an binne dan bangar, Yayin da Sojoji, ‘yan sanda da ‘yan banga sun zo wurin. Suna cikin daji yanzu suna neman ‘yan ta’addan kuma suna kokarin ceto wadanda aka sace,” in ji majiyar.

Sai dai kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Josephine Adeh, ya ci tura, haka kuma lambar wayar ta baya shiga, har zuwa hada wannan rahoto.

A yan kwanakin nan rahotanni makamantan wannan kan sanya tsoro da razani a zukatan Al’umma, ganin yadda shiyyoyi da jihohi ke fuskantar kalubale da ya shafi tsaro da garkuwa da mutane.

Batun samar da tsaro kan fito a jawabai da Uwargida Oluremi Tinubu kan gabatar a cikin jawabai, a makon da ya gabata ta shaidawa majalisar sarakunan jihar Ekiti cewar mai Gidanta  yana iyakacin kokarinsa wajen ganin an kawo karshen matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *