Aljeriya ta kaddamar da na ta bangaren na aikin shimfida bututun Iskar gas na (Trans-Saharan Gas Pipeline TSGP), da zai tashi daga Najeriya ya shige ta Nijar zuwa kasar Aljeriya.
Mahukuntan kasashen Uku sun yi wata ganawa a ranar Alhamis 4 ga watan Yuni, a yankin In Guezam dake Lardin Tamanrasset akan iyakar Nijar da Aljeriya.
Karamin Ministan Man Fetur na Aljeriya Mohamed Arkab da takwaransa na Nijar Hamadou Tinni, da kuma Karamin Ministan Albarkatun Fetur da Iskar Gas na Najeriya Honarabul Ekperikpe Ekpo ne suka wakilci kasashen nasu.
Shafin Fitilar Nijar ya ruwaito cewa kasashen biyu sun kaddamar da aikin shimfida bututun, da zai taso daga Najeriya ya ratsa ta Nijar zuwa Aljeriya, da nufin Dillancin Makamashin Iskar ga kasashen Turai.
Najeriya na sa ran tunkuda biliyan 20 zuwa 30 na Iskar gas a kowacce shekara zuwa Aljeriya, wanda a karshe zata yi dillancin sa zuwa kasashen ketare .

Yarjejeniyar farko ta nuna cewar kasar Aljeriyar ce ta amince ta bayar da dukkanin damar amfani da na’urori da kayan aikin da kuma kwarewar data ke dashi, domin ganin kasashen 3 sun cimma wannan buri.
Tun a farkon Shekara ta 2000 ne aka fara wannan shiri, sai dai ya fuskanci tsaiko sakamakon matsaloli na kudin aiwatar dashi.
Sai dai batun ya sake tasowa a wannan lokaci da kasashen Yamma ke fuskantar karancin makamashin Iskar Gas sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya, da kuma tsamin dangantaka da Kasar Rasha.
