Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa zai yi wa al’ummar Kasar jawabi da karfe 6:00 na Maraicen Ranar Lahadi.
Gidan Talabijin na kasar CNBC ne zai haska Jawaban Shugaban kai tsaye, kuma zai mayar da hankali ne kan matsayin kasar ga bakin hauren dake zaune cikin ta ba bisa ka’ida ba.
Har Ila yau kafar tace Jawaban Shugaban zasu tabo karuwar zanga-zangar kyamar baki da ke cigaba da yaduwa a Sassan kasar.
Ana sa ran shugaban zai bayyana sabbin matakan da gwamnati za ta dauka game da wannan batu, da Kasashen Nahiyar ke yiwa kallon bakon al’amari
A ranar Lahadi 7 ga watan Yunin 2026 ne Gwamnatin Najeriya ta fidda sanarwar cewar ta kammala tantance yan kasar ta dake zaune a Afirka ta Kudu, da nufin dawo dasu gida.
Tuni kasashe irinsu Ghana da Mali da Uganda suka kammala kwashe nasu yan kasar, kusan makonni biyu zuwa uku da suka gabata.
Zangar-Zangar dai na neman rikidewa daga nuna damuwa kan yadda yan Afirka ta kudu ke cewa baki sun mamaye dammamakin ayyuka a kasar su, zuwa wani al’mari ta hanyar kai farmaki kan yan masashen waje.