Rasuwar Matashin ta sanya jimami a zukatan al'ummar Unguwar Rogo.

Wani matashi da aka bayyana sunan shi da Salisu Muhammed ya rasu bayan ya fadi a lokacin Atisayen Kwallon Kafa da safiyar ranar Litinin a Birnin Jos.

Lamarin ya faru ne a filin wasa na Masallacin Idi da ke cikin Unguwar Ali Kazaure, dake Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Wani abokin wasan mamacin, Abba Abdullahi, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa Muhammed na cikin Atisayen kawai sai suka ga ya fadi ba zato ba tsammani.

“Mutuwa ce mai ban mamaki. Yana buga kwallo ne sai kawai ya fadi. An garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji Abba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mamacin mai lakabin “Achilata” mazaunin Unguwar Rogo ne, kuma rasuwar sa ta sanya jimami a zukatan abokai da yan uwa, iyaye da kuma matarsa mai ‘ya’ya hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *