Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana shirin gabatar da kudirin doka da zai samar da wa’adi guda na shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni.
A cewar Bamidele, yana son gabatar da kudirin da zarar ya sake dawowa wakilci bayan zaben shekarar 2027.
Ya kara da cewa kudirin dokar zai kasance cikin kudirorin farko da yake shirin gabatarwa idan aka kaddamar da majalisar dattawa ta gaba ta 11.
-
Sabon Ofishin EFCC Zai Ƙarfafa Yaƙi da Cin Hanci — Tinubu
-
Matukar zamu hada kan mu, matsalar tsaro zata kau-Pantami
Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa ranar Talata, dan majalisar ya ce masu rike da mukami na amfani da wa’adin su na farko na tsarin wa’adi biyu na yanzu don lissafin siyasa da shirye-shiryen neman tazarce.
“…idan muka dawo a majalisar dattawa ta 11, in Allah Ya yarda, zan gabatar da kudirin da zai sa duk wanda ke son zama shugaban kasa ko gwamna, ya yi wa’adi guda kawai na shekara shida,” in ji shi.
A cewarsa, wa’adi guda zai kawar da duk wata matsala da ke tattare da neman wa’adi na biyu.
“Idan ka san kana nan na shekara shida, wa’adi guda kawai, za ka saka dukkan karfinka tun daga ranar farko. Ka san wannan ce kadai damar da kake da ita.”
Sai dai kuma kudirin idan aka gabatar da shi a hukumance kuma majalisar dokokin kasa ta amince da shi, zai bukaci gyaran kundin tsarin mulki kafin ya fara aiki.