A kalla Mutane 34 suka rasa rayukansu a watan Mayun 2026 sakamakon hatsarin mota a Jamhuriyar Nijar, yayin da mutane 209 suka samu munanan raunuka.

mutane 522 suka samu ƙananan raunuka, kamar yadda alkaluman hukumar ‘yan sanda suka nuna.

Shafin facebook na Fitilar Nija ya ruwaito cewa  kimanin hadurra 1,198 aka yi wa rajista a watan Mayu, adadin da ya fi na watan Afrilu, inda aka samu hatsura 1,103.

Birnin Niamey ne ya kasance kan gaba wajen yawan hadurra, yayin da Tahoua ta zo ta biyu, a cewar jami’ai.

Bincike ya nuna cewa rashin bin ƙa’idodin tuki, tukin  ganganci, amfani da waya yayin tuki, da kuma tuki a cikin yanayin maye na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yawaitar hatsuran ababen hawa a Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *