Shugaban yayi kira ga matasa su tashi tsaye wajen kare Dimukradiyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wasu fitattun masu fafutukar dimokuraɗiyya lambobin yabo na ƙasa saboda rawar da suka taka wajen ci gaba da gwagwarmayar dimokuraɗiyya a Najeriya

Shugaban ya bada lambobin yabonne  yayin jawabin da ya gabatar a ranar 12 ga Yuni domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026

Waɗanda aka karrama sun haɗa da Manjo Janar M.A. Garba, Birgediya Janar Lawal Jaafaru Isa, Kanal Umar Farouk Ahmed, Kanal Sambo Dasuki, Kanal Lawan Gwadabe, Birgediya Jonathan Ndam Temlong, Manjo Janar Chris Eze da Birgediya Yahaya Abubakar.

Tinubu ya bayyana tsaffin sojojin da “sojojin dimokuraɗiyya”

Shugaban ya kuma karrama  Barrista Ayoka Lawani, Tunde Fagbenle, Oladele Alake, Olatunji Bello, Louis Odion, Segun Babatope, Sam Omatseye, Bola Bolawole, Debo Adeniran.

Sauran sun hadar da Cif Ayo Opadokun, Farfesa Sylvester Odion-Akhaine, Dakta Joe Okei-Odumakin, Richard Akinnola, Manjo Janar Ishola Williams (mai ritaya), Femi Aborisade, Gbemiga Ogunleye da Babajide Kolade-Otitoju.

Tinubu ya ce za a fitar da cikakken jerin sunayen waɗanda aka ba lambobin yabo a cikin kwanaki masu zuwa.

yanci da dimokuraɗiyya sun samar da ci gaba da walwala ga kowa.

Ya kuma sanar da cewa za a sauya sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur da Gas ta Kaduna (Institute of Petroleum Studies) domin girmama marigayi Shehu Musa Yar’Adua.

Shugaban ya yi jinjina ga fitattun jaruman gwagwarmayar dimokuraɗiyya da suka haɗa da M.K.O. Abiola, Alhaja Kudirat Abiola, Gani Fawehinmi, Bola Ige, Alfred Rewane, Pa Abraham Adesanya, Anthony Enahoro, Alhaji Balarabe Musa, Commodore Dan Suleiman, Dakta Beko Ransome-Kuti, Frank Kokori, Arthur Nwankwo da Chima Ubani.

Tinubu ya bayyana cewa ranar 12 ga Yuni ta ci gaba da zama alamar haɗin kai ga ‘yan Najeriya, inda ya buƙaci jama’a, musamman matasa, da su kare dimokuraɗiyya, su ba da gudummawa wajen gina ƙasa, tare da tabbatar da cewa ‘yanci da dimokuraɗiyya sun samar da ci gaba da walwala ga kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *